Sports Betting

Trending

random

Jonathan na taya matasan Najeriya murna

–Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan na kira ga matasan najeriya su cigaba da jajircewa akan samun nasara

– Tsohon Shugaban kasan ya mika sakon ne domin taya murna a ranar matasan duniya

Tsohon shugaban kasan najeriya, Goodluck Jonathan ya taya matasan najeriya murna a zagayowar ranan matasan duniya. Wannan ran ace wadda majalisar dinkin duniya ta kebance domin taya matasa masu tsakatsakin shekaru murna.

Jonathan 4

Jonathan ya bayyana hakan ne ta shafin sada zumuntar sa ta Facebook , ya hakaito wasu bangarorin da matasan Najeriya suka taka rawan gani a cigaban kasa ,kuma yana kira da su cigaba da taimakama kan su.

Ya ce : “Ina sara ma jajircewa da kokarin matasa a rana irin ta yau da aka kebance musu. Daga Adichie zuwa Jelani Aliyu, matasan mu sune abin Alfaharin mu. A lokacin da tattalin arzikin mu ya zama na daya a nahiyar afrika, saboda matasan mu ne. Lokacin muka yi wuta a gasar Olympics da wasu wasanni, saboda matasan mu ne.

 “Najeriya bata da wani abun alfahari fiye da matasan ta kuma sune abin da ke kara mini karfin guiwa. Sako na zuwa matasa shine su cigaba da bunkasa kansu ta kowani fanni, Allah albarkaci matasan mu GEJ”.

KU KARANTA : Matasan jam’iyar PDP sun kai wa dan majalisa hari

Tun lokacin da tsohon shugaba jonathan ya bar ragamar mulki a 2015, ya cigaba da ayyukan kawo zaman lafiya a Afrika ,kana ya kirkiro kungiyar Goodluck Jonathan Foundation. A kwanakakin baya, Goodluck ya jagoranci tawagar kungiyar gamayyar nahiyar Afrika wajen duba zaben kasar Zambia da aka yi ranan 11 ga watan Augusta.

 

 

 

 

The post Jonathan na taya matasan Najeriya murna appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.


Jonathan na taya matasan Najeriya murna Reviewed by Olusola Bodunde on 04:40 Rating: 5

No comments:

Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us

All Rights Reserved by Naija News Live © 2014 - 2015
Powered By Blogger, Designed by Sweetheme

Contact Form

Name

Email *

Message *

Powered by Blogger.