Shugaba Buhari ya mika sakon murna ga yan wasan Najeriya
–Shugaba Buhari yayi kira ga yan kwallon najeriya da su dawo da kofin zinari a wasan gasar Olympics din da ke gudana a Rio
–Buhari yayi kira ga yan Najeriya da su goyi bayan yan wasan Najeriya
A daren jiya ne ,13 ga watan Augusta, Shugaba Buhari ya yabawa yan kwallon Najeriya da ke fafatawa a gasar Olympics bayan sun lallasa kasar Denmark domin karasawa wasan kusa da karshe a gasar.
Mikel
Buhari ya tunada cewan ba’a mayar da hankali kan yan wasan ba kafin gasan . amma yana nuna fain cikin sa akan nasarar su zuwa wasan kusa da karshe ,yana kira dasu su dawo da kofin zinari.
Ya fadi ta mai Magana da yawun shugaban kasa, femi adesina: “Kuma , wannan ruhun nasara na yan najeriya na cigaba . Wannan yan kwallo ne da ba’a mayar da hankali kan sub a, amma sun karasa wasan semi-final. Ku ciwo zinarin, kuma a daga tutar Najeriya a duniya.
Shugaba Buhari yayi kira ga yan Najeriya da su taimaka ma yan wasan da addu’a domin samun nasara musamman yan kwallon.
KU KARANTA : Rio Olympics: Kasar Spain ta doke Nigeriya wajen kwallon kwando
“Saboda duniyan ta sani cewan duk da durkushewar tattalin arzikin mu, ruhin najeriya bata fadi ba.”
Kaftin din yan wasa, John Mikel Obi da Aminu Umar ne suka saka kwallo a ragan kasar Denmark domin haduwa da kasar Jamus a wasan semi-final
The post Shugaba Buhari ya mika sakon murna ga yan wasan Najeriya appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
No comments:
Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us