Sports Betting

Trending

random

Sana’a sa’a: Ku karanta labarin wata mace mai sana’ar walda a jihar Delta

Wata matashiya mai shekaru 23 a duniya kuma mai suna Happiness Ozoalor itace mace daya tilo dake sana’ar walda a jihar Delta. Ita dai wannan matar yar asalin jihar Enugu ce amma kuma an haife tane a garin Aniocha a shekarar 1993.

Wakilin Naij.com ya ziyarci matar a shagon sana’ar ta dake a kan titin Onisha/Benin daura da filin jirgi na garin Asaba inda ya tarar da ta baza hajar ta tana jiran masu saye. Matar ta shaida mana cewa a da tayi aiki ne a wani kamfanin in man gashi amma sai ta koma yin sana’ar walda saboda sha’awar ta da takeyi kemanin shekaru 5 da suka wuce.

share (31)

Ita dai wannan matar ta shaida ma na cewa ta kammala karatun ta na sakandire a wata makaranta mai suna Gateway to Success a garin Ebu na karamar hukumar Oshimili ta arewa kafin daga baya ta fara koyon aikin walda a tsakanin shekara ta 2012 zuwa 2013 a hannun wani Mr. Emeka Isichei.

Matar ta kuma bayyana mana cewa bata samu matsala da iyayenta ba wajen fara sana’ar. Basu takura mata ba ko kadan ganin cewa kowa yasan sana’ar maza ce.

share(3) (1)

Mahaifin matar dai ya mutu ne a shekara ta 2014 wanda shine ma dalilin su na dawowa Enugu a cewar ta. Ta cikigaba da cewa kasantuwar itace diya ta farko a wajen mamar ta shine ma ya sanya ta dole ta nemi sana’ar yi don ta tallafawa mamarta da kuma kannen ta.

Duk da cewa ita kadaice macen da keyin walda a garin na Delta, hakan bai sa na zama wata saniyar ware ba don kuwa yanzu haka ma ita ce jami’ar walwala da jin dadi ta kungiyar yan walda ta jihar Delta din.

share(4) (1)share(2) (1)

Matar ta kuma ci gaba da cewa ina da tabbacin cewa wannan sana’ar duk da sauran mata zasu ga kamar tana da wahala kokuma bata dace da ita ba, a ganin ta tafi karuwancin da dayawan su ke shiga kuma suka maida sana’a.

The post Sana’a sa’a: Ku karanta labarin wata mace mai sana’ar walda a jihar Delta appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.


Sana’a sa’a: Ku karanta labarin wata mace mai sana’ar walda a jihar Delta Reviewed by Olusola Bodunde on 09:20 Rating: 5

No comments:

Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us

All Rights Reserved by Naija News Live © 2014 - 2015
Powered By Blogger, Designed by Sweetheme

Contact Form

Name

Email *

Message *

Powered by Blogger.