Sports Betting

Trending

random

Rio Olympics: Tawagar Najeriya ta sake ‘kwafsawa’

Har ilayau dai tawagar yan wasa daban daban da ta wakilci kasar Najeriya wajen gasar Olympics ta kara kwafsawa inda ta sanya kayan atisaye a maimakon kayan gargajiya a lokacin bukukuwan bude gasar da aka gudanar a garin Rio na kasar Brazil.

Rahotanni dai sun nuna cewar kasar ta Najeriya bata bada kayan gargajiyar ba cikin lokaci wannan ne dalilin da yasa ba su sa su ba. Sauran kasashen Afirikan da suka je gasar dai duk da kayan gargajiyar su suka yi bukin bude gasar.

Team Nigeria at the Opening ceremony of the RIo Olympics

Team Nigeria at the Opening ceremony of the RIo Olympics

Shahararren dan kwallon tebur din nan na kasar Najeriya wanda kuma shine ke wakiltar kasar a fagen wasan tebur dai ya dauki tutar kasar lokacin bukukuwan budewa.Mai karatu dai zai iya tuna cewa yan kwallon kasar ma dai sun makara sosai wajen isa birnin na Rio sakamakon rashin kudin jirgi da babu.

The post Rio Olympics: Tawagar Najeriya ta sake ‘kwafsawa’ appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.


Rio Olympics: Tawagar Najeriya ta sake ‘kwafsawa’ Reviewed by Olusola Bodunde on 09:04 Rating: 5

No comments:

Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us

All Rights Reserved by Naija News Live © 2014 - 2015
Powered By Blogger, Designed by Sweetheme

Contact Form

Name

Email *

Message *

Powered by Blogger.