Sports Betting

Trending

random

Wasannin da ake sa rai Nigeria za ta yi rawar gani a Rio

Bayan rashin tabuka komai a gasar guje-guje da tsalle da tsalle Na Olympics da aka yi London a shekarar 2012 a inda ta Nigeri ta gaza cin lambar zinare ko daya, wannan karon fatan ganin cewa kasar za ta yi rawar gani a wasan gasar Rio musamma wasu wasanni 5

Ba yabo, ba fallasa a shirye-shiryen Nigeria zuwa gasar Olympics a wannan shekara ta 2016 a Rio ba zai zama kasha dari bisa dari ba, sai a baya kasar ta nuna cewa idan ta fada cikin matsi kasar ta fi yi rawar gani.

Team Nigeria flops at the opening ceremony of the Rio Olympics

Tawagar Nigeria a bikin bude gasar Rio Olympics

Nigeria na da ‘yan wasan nagartattun ‘yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle wadanda za su iya gogayya da takwarorinsu na duniya kamar yadda ta tabbata a karawar kasar da Japan a wasan kwallon kafa, a inda Najeriyar ta lallasata da ci 5 da 4. Ganin haka ne ya sa ake yi wa kasar hasashen cin lambar Zinare a wadannan wasanni kamar haka:

1. Gudun mita 100 da 200 da kuma wasan tsalle daya

Mace daya da ta yi fice a gasar tseren mita 100 da 200 ita ce Blessing Okagbare, kuma ita ce ake sa rai za ta fidda kasar kunya. Abokiyar kalu-balenta a wannan gasa ita ce Shelly-Anna Fraser Pryce ta kasara Jamaica.

KU KARANTA: Tsohon dan kwallon Najeriya Ogaba ya mutu

2. Tseren karba-karba

A gasar wasannin Olympics na baya, Nigeria ta kasance a kan gaba wajen gasa da manyan kasashe a wannan tsere a inda Okagabare ke wakailtar Nigeria tseren 4 sau 100.

3. Kokawa

Ana sa rai Odunayo Adekuoroye za ta taka rawar gani a wannan nau’in kokawar ta mata. Domin ta zama zakara a gasar ta india, ta kuma cin Zinare a wasan kungiyar kasashe renon Ingila watau Commonwealth games a Glasgow ta Scotland.

 

 

 

 

The post Wasannin da ake sa rai Nigeria za ta yi rawar gani a Rio appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.


Wasannin da ake sa rai Nigeria za ta yi rawar gani a Rio Reviewed by Olusola Bodunde on 08:48 Rating: 5

No comments:

Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us

All Rights Reserved by Naija News Live © 2014 - 2015
Powered By Blogger, Designed by Sweetheme

Contact Form

Name

Email *

Message *

Powered by Blogger.