Sports Betting

Trending

random

Abu 5 da ya taimaka ma Najeriya a wasan su da Japan

Tabbas Najeriya ta lallasa kasar Japan a wasan su na farko da suka buga a garin Rio. Dukkan dan Najeriyar ma da ya kalli kwallon ma abun ya burgeshi sosai.

Hakan ne ma yasa har masana kwallo sun fara cewa idan dai har suka cigaba da kwallo a haka to tabbas za su iya lashe gasar.

Ga dai abubuwa 5 nan da muka zakulo maku wadanda suka taimakawa kasar Najeriya sosai a wasan:

 

1) Dan wasa Mikel da ya rika zuwa gaba yana taimakawa dan kwallon gaban kasar Etebo. Haka ma wannan ne yasa Sadiq Umar shima ya rika watawa sosai a cikin filin yana takurawa yan kwallon Japan din.

 

2) Yan Najeriya sun rarraba kwallon yadda ya kamata: yadda yan kwallon Najeriya suka rika rarraba kwallon suna fasin ta ko ina ma dai ya taimaka sosai don kuwa kusan rudar da tawagar ta Japan ma sukayi.

 

3. Yan Najeriya akwai karfi: to ai koma ba’a fada ba daman yan nahiyar Afirika akwai karfi musamman ma idan aka kwatanta su da yan nahiyar Asiya irin kasasen Japan. To wannan karfin ma dai yayi anfani sosai.

 

4. Suma yan bayan Najeriya basuyi kokari ba: rashin kokarin da yan bayan Najeriya sukayi shine ma ya sa har kasar Japan din ta zura kwallaye har 4 itama. Duk da kokarin da yan Najeriya sukayi a gaba da kuma tsakiya, sai yan bayan sukayi bacci su kuma.

 

5. Yan Najeriya sun nuna kwarewa: tun daga ma yadda Mikel ya nuna jarumta wajen kwallon har zuwa yadda kuma ya nuna rashin son kai inda ya dauko kwallo yaba dan wasan gaban Najeriya Etebo ya buga fenaraty wanda kasar ta samo.

The post Abu 5 da ya taimaka ma Najeriya a wasan su da Japan appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.


Abu 5 da ya taimaka ma Najeriya a wasan su da Japan Reviewed by Olusola Bodunde on 09:04 Rating: 5

No comments:

Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us

All Rights Reserved by Naija News Live © 2014 - 2015
Powered By Blogger, Designed by Sweetheme

Contact Form

Name

Email *

Message *

Powered by Blogger.