Sports Betting

Trending

random

PDP Bata Bani Cin Hancin Naira Miliyan 700 Ba – Kwamishinan Zabe Na Rivers

Kwamishinan zabe na Jihar Rivers, Gesila Khan ta musanta zargin da Jam’iyyar APC take yi mata cewa wai PDP tayi kokarin bata cin hancin Naira Miliyan 700.

Jaridar The Sun ta ruwaito cewa, lauyan kwamishiniyar zaben, Selkeowei Larry (SAN) ne ya musanta zargin na cin hancin da aka yi mata a garin Abuja.

Gesila Khan ta kalubalanci Jam’iyyar APC ta bada cikakken bayanin akawunt din da ake zargin an saka  kudin. Tace ita bata dauki bangare ba a matsayinta na ma’aikaciyar hukumar zabe. Tace duk abunda tayi, yayi daidai da bukatar dokar kasa.

Khan tace wanna zargin da akeyi mata ba shida tushe, kuma ana kokari ne  kawai a bata mata suna. Kwamishiniyar zaben ta Rivers ta nunan rashin jin dadin ta yadda yan jarida sukayi saurin buga labarin zargin da akeyi mata ba tare da sun nemi abasu shaidar dake nuna hakan ba.

Tace: “Ban taba ansar cin hanci ba. Bani da irin wannan kudin. Ina kalubalantar Jam’iyyar APC ta fiddo da cikakken bayani da ke nuna cewa an bani Sanya kudin a akwunt dina.”   

Khan tace miyakon a ringa sanya mata albarka akan bautar da tayi ma kasarta, anzo ana tsangwamarta. Inda suke magantawa akan batun bayan da jam’iyyar yan sanda masu farin kaya suka fara bincikar Khan, Jam’iyyar APC ta jihar tace ma khan ta bayyana Inda ta samu Naira miliyan 700.

The post PDP Bata Bani Cin Hancin Naira Miliyan 700 Ba – Kwamishinan Zabe Na Rivers appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.


PDP Bata Bani Cin Hancin Naira Miliyan 700 Ba – Kwamishinan Zabe Na Rivers Reviewed by Olusola Bodunde on 07:27 Rating: 5

No comments:

Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us

All Rights Reserved by Naija News Live © 2014 - 2015
Powered By Blogger, Designed by Sweetheme

Contact Form

Name

Email *

Message *

Powered by Blogger.