Sports Betting

Trending

random

Ambaliyan ruwa ta tafi da wani dan shekara 60 a Osogbo

– An ga gawan Elder Ebenezer Olabode, wanda ambaliyan ruwa ta tafi da shi a kan rafin Okooko a goben ranan a Oke Oniti na jihar  Osun

– An ce mutumin da hanyar dawowa gida ne ruwa ta shanye shi

Flood after rain

An ga gawan Elder Ebenezer Olabode, wanda ambaliyan ruwa ta tafi da shi a kan rafin Okooko a a yammacin ranan talata,13 ga watan Satumba, a ranan laraba a Oke Oniti na jihar Osun.

Nigerian Bulletin ta bada rahoton cewa mutumin na dawowa gida ne ambaliyan ruwa ta shanye shi a kusa da gidan shi.

Game da cewar idon shaida,Olabode yay i karfin halin shiga cikin ambaliyan bayan mutane sun bashi shawaran cewa kada ya shiga ciki. Idon shaidan mai suna, Thomas Onaolpo ,yace hausawan da ke wurin sun kasa ceto shi bayan an kwashe awanni ana yi.

KU KARANTA:DUMI-DUMI: Shugaban Tsageru ya shiga hannun Sojin Ruwa

Yace: “Mun yi masa gargadin kada ya shiga ya ki ji. Bayan ya dan fara shiga, sai ruwa ya fara shiga bayan motarsa . wani mutumi da yayi kokarin ceton sa shima ya kusa bin ruwa,sai muka hakura muka barshi. An ajiye gawanshi a dakin ajiye gawawwaki a asibitin Asubiaro.

Bisa ga ruwan sama, wani labara mai kama da haka ya faru a Aba, jihar Abia ,a ranan talata,13 ga watan Satuma, yayinda aka ga gawan mutumin saman ruwa wajen kasuwan Ariaria.

Game da hoton, an ga gawan mutumin amma ba’a san daga inda yake ba.

The post Ambaliyan ruwa ta tafi da wani dan shekara 60 a Osogbo appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.


Ambaliyan ruwa ta tafi da wani dan shekara 60 a Osogbo Reviewed by Olusola Bodunde on 07:39 Rating: 5

No comments:

Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us

All Rights Reserved by Naija News Live © 2014 - 2015
Powered By Blogger, Designed by Sweetheme

Contact Form

Name

Email *

Message *

Powered by Blogger.