Manyan Labarai Guda 7 Da Sukayi Fice A Ranar Laraba
Naij.com ta tattara maku manyan labarai guda 7 wadanda sukayi fice a ranar Laraba 16 ga watan Agusta, ku duba domin samun su.
1. Hukumar CCB ta bayyana laifuka 13 na rashawa da Saraki yayi.
Hukumar CCB ta bayyana laifuka na rashawa da almundahana wadanda Shugaban Majalisar Dattawa yayi a lokacin da yake gwamnan Jihar Kwara.
2. Shugaba Buhari ya nada Dominic Abonyi.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nada Dominic Abonyi a matsayin Rajistara na ma’aikatan lafiyar muhali.
3. Gwamna Nasiru El Rufa’i ya kulle Coci 2, da makarantar Coci.
Gwamnan Jihar Kaduna ya bada umurni a kulle Coci guda 2, da makarantar Coci guda 1 a karamar Saminaka dake Jihar Kaduna.
4. Shugaban Kasa Buhari Ya dawo Najeriya.
Shugaban Kasa Buhari ya dawo Najeriya daga ziyarar da ya kai ma Faransa ta kwana 3.
5. Hukumar hana almundahana na neman dan tsohon dan takarar shugban kasa.
Hukumar EFCC na neman tsohon dan takara shugaban kasa a karkashin jam’iyyar Nigeria’s liberation Party, Emmanuel Osita Okereke.
6. Shugaba Buhari yayi fira da France 24
Shugaban Kasan Najeriya yayi fira da gidan Talabijin na France 4 inda suka tattauna akan zaben ministocin shi,Boko Haram d.s.s
7. Sojojin Najeriya sun kama Yan Boko Haram
Sojin Najeriya sun amshi wasu yan Boko Haram da suka tuba a Jihara Adamawa wanda yawan su yafi sama da 200.
Note: There is a poll embedded within this post, please visit the site to participate in this post's poll.The post Manyan Labarai Guda 7 Da Sukayi Fice A Ranar Laraba appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.
No comments:
Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us