Sojojin Najeriya Sun Kama Wata Yar Kunar Bakin Wake
Sojojin Najeriya sun kama wata yar kunar bakin wake a jihar Borno. Mukaddashin Darakta mai kula da labarai Kanar Sani Usman ne ya bayyana haka.
Sojojin Najeriya
Yace: “Da kimanin karfe 8:00 na safe, wasu yan mata suka kai hari a Madagali inda suka kashe mutane 17, sannan kuma 44 suka raunata.
“Shima kwamandan sojojin na Dibishan ta 7, Manjo Janar Lamidi Adeosun, yayi karin bayani inda ya bayyana cewa mutane 26 ne suka rasa ratukan su. Sanna ya bayyana cewa mata yan kunar bakin wake 14 ne sukayi kokarin kaima Maiduguri hari inda Sojoji suka hana su.”
Ya bayyana cewa sunyi kikarin kai harin ne ta hanyoyi guda 4; Asuwari, Mulai, Kura Baderi dake hanyar Damboa. Amma sai sojoji suka tare su inda ukku suka fashe suka kashe mutane 26.
Sojoji sun kashe 10 daga vikin su inda 3 suka ruga suka tada Ban din. Daya taje wani gida inda ta roki a bata butavtayi alwalla sai taje kusa da wani massallaci ta tada Bam din.
Kwamandan ya yaba ma sojojin inda ya bayyana cewa zasu kawo karshen ta’addanci. Daya daga cikin matan Fatima ta bayyana cewa ada tana zaune a Bullukuntu a Abuja, sannan kuma tana da diya guda Daya. Ta bayyana cewa an kawo su Munguno inda aka aje su tare da yan Boki Haram.
The post Sojojin Najeriya Sun Kama Wata Yar Kunar Bakin Wake appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.
No comments:
Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us