Buhari Ya Nada Sabon Shugaban NDLEA
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya amince da nada Laftanan Kanar Muhammad Abdullahi a matsayin sabon shugaban NDLEA (hukumar hana fataucin miyagun kwayoyi).
Wannan ya fito ne daga bakin Sakataren gwamnati, Babachir Lawal inda ya bayyana cewa an nada Muhammad ne a ranar 11 ga watan Janairu 2016.
Muhammad yayi karatu a fannuka daban daban inda yayi karatu a NDA, Amurka sannan ya karanci Shari’a a Najeriya a 2006.
Sannan kuma hukumar tayi jinjina ga tsohon shugaban hukumar Giade akan kikarin da yayi ma hukumar bayan daya shugabance ta har tsawon shekara 10.
The post Buhari Ya Nada Sabon Shugaban NDLEA appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.
No comments:
Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us