An kori sojoji saboda kin yin pareti
Sojoji kimanin 250 ne aka kora daga Bariki na Jaji dake a Kaduna saboda kinyin pareti. Sojojin ne suka bayyana haka inda suka ziyarci zauren yan jarida a Kaduna.
Sun bayyana cewa suna cikin sojoji dubu ukku wadanda aka maido dasu bakin aikin su bayan da aka kore su. Sunyi kimanin watanni Ukku suna shan gwaje gwaje, sai a ranar karshe ne basu da wurj ba sai aka kore su.
Jaridar Daily Post ta ruwaito cewa wani soja ya bayyana cewa sunzo wajen yan jarida ne domin suyi kira ga shugabannkasa da kuma hukumar soji da ayi masu afuwa kuma a maida su bakin aikin su.
Sun bayyana cewa a ranar 1 ga watan Fabrairu ne hakan ta faru kuma har zuwa yanzu ba’a kira su ba. Shugabannin Jaji sun bayyana cewa baza su maganta a yanzu ba, amma su tabbatar da cewa hukumar soji zata maganta kuma zata sanar da mutwne a’inafin abunda ya faru.
The post An kori sojoji saboda kin yin pareti appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.
No comments:
Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us