Sports Betting

Trending

random

Hukumar kwallon kafan Najeriya ta soke garabasa

Hukumar kwallon kafar Najeriya watau Nigeria Football Federation (NFF) tace ba zata kara biyan yan kwallo ba da kudin dola. Daga yanzu dai za’a rika biyan yan wasanne bayan duba da irin kokarin da suka yi a duk wasa kamar dai yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Nigeria Football Federation

Nigeria Football Federation

Hukumar ta cimma wannan matsayin ne dai bayan shawarwarin da wani kwamitin ta ya gabatar mata a Abuja. Sabbin shawarwarin da aka gabatar dai zasu fara aiki ne daga wasannnin share fagen shiga gasar kasashen duniya da za’ayi a kasar Russia 2018.

Wannan yana nuna cewa a wasannin masu zuwa ba za’a bada kudaden garabasar ba bayan duk wasa. Sabanin haka, hukumar zata biya yan kwallon ne idan har sun samu tikitin shiga gasar. Kuma hukumar tace zata biya yan wasan ne da kudin Naira a duk wasan da suka buga a nan gida.

Ku karanta: Messi ya kafa tarihi

Majiyar mu ta bayyana mana cewa ya zuwa yanzu dai hukumar ta bayyana cewa: “duba da yadda tattalin arzikin kasar yake, ba zamu iya biyan ko wane dan wasa garabasar $10,000 akan ko wane wasa ba ko da kuwa anyi nasara ko kuma ba’ayi ba.”

“Yanzu zamu rika biyan yan wasan ne dai dai da kokarin su a kowane wasa kamar dai yadda akeyi sauran kasashen duniya.”.

Haka madai wata shawarar da aka gaba tar itace su kuma yara masu bugama kasar kwallo watau Golden Eaglets, za’ rika ba su kudin su ne a kudin Naira kawai.

The post Hukumar kwallon kafan Najeriya ta soke garabasa appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.


Hukumar kwallon kafan Najeriya ta soke garabasa Reviewed by Olusola Bodunde on 08:01 Rating: 5

No comments:

Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us

All Rights Reserved by Naija News Live © 2014 - 2015
Powered By Blogger, Designed by Sweetheme

Contact Form

Name

Email *

Message *

Powered by Blogger.