Sports Betting

Trending

random

Jamie Vardy ya ki yadda da tayin Arsenal na £150,000

Dan wasan gaban kasar ingila Jamie Vardy ya ki yadda da tayin £150,000 duk sati daga kulob din Arsenal yayin kuma da ya amince da kara kwantaragin sa da kulub din sa na Leicester City har na tsawon shekara 4

Jamie Vardy

Jamie Vardy

Kulob din na Leicester zai rika bashi £100,000 a duk sati. Kulob din na Arsenal dai ya bukaci siyan dan wasan wanda shi kuma ya ki amincewa da hakan don fargabar rashin samun isassen lokacin buga wasa a kulob din.

Verdy dai ya zura kwallaye 24 a kakar wasan da ta wuce.

Wata sanarwar da aka fitar ta ce: “Yau Alhamis kulob din Leicester City tare da wakilin Jamie verdy ya amince da ya sabunta kwantaragin sa da kulob din har na tsawom shekarun 4.”

“Duka ban garorin biyu na fatan wannan zai kawo karshen rade raden da ake yi game da makomar dan wasan don kuma ya yarda ya tsaya a kulob din nasa.”

Ana sa nan Arsenal din zata maida hankalin ta wajen neman Alvaro Morata amma kuma kulob din sa na Real Madrid baza su anshi kasa da kudi £40m ba.

The post Jamie Vardy ya ki yadda da tayin Arsenal na £150,000 appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.


Jamie Vardy ya ki yadda da tayin Arsenal na £150,000 Reviewed by Olusola Bodunde on 08:01 Rating: 5

No comments:

Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us

All Rights Reserved by Naija News Live © 2014 - 2015
Powered By Blogger, Designed by Sweetheme

Contact Form

Name

Email *

Message *

Powered by Blogger.