Sports Betting

Trending

random

Kungiyar OYC sun gargadi Niger Delta Avengers

-Kungiyar OYC sun bukaci kungiyar Niger Delta Avengers da su karbi tayin tattaunawa kuma kada su gudanar da harin bom da suke barazanar yi

-An ce ba’a kama ko wani mamba na kungiyar IPOB ko MASSOB ba a jihar

-Kungiyar ta yaba ma gwamna Okezie Ikpeazu kan aikin shi a jihar

Tsageru

Tsageru

Kungiyar Ohaneze Ndigbo Youth Council (OYC) sun yi gargadi ga tsagerun Niger Delta Avengers da kada su kai harin bom da suke barazanar yi a jihar Abia da kuma ko wani yanki a kasar.

Kungiyar yan’bindiga da suke da alhakin saka bama-bamai a bututun mai a yankin Niger Delta sun yi barazana ga gwamnoni bakwai, da su saki masu yakin Pro-Biafra wanda yan’sanda da sojoji suka tsare a jihohin su, ko kuma su fuskanci fushin yan’bindigan.

KU KARANTA KUMA: Gwamnonin Niger Delta na aiki da yan’bindiga – Itsekiri

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa a wata jawabi da Isreal Ogbonnaya da Chetachi Ike wadanda suka kasance shugabanni a sakateriyan jihar Abia, sun ce, matasa sun bukaci tsagerun da suyi na’am da tattaunawa da gwamnati.

“Muna kira ga yan kungiyar Niger Delta Avengers da su ajiye makaman su da kuma ajiye kudurin sun a barazanar saka bam a jihar Abia da sauran jihohi.”

Kungiyar OYC sun kuma yaba ma gwamna Okezie Ikpeazu da kulawa da rancen naira biliyan daya a harkan noma a jihan, sun kuma bukaci da ya cika alkawarin shi na cewa za’a ba ingantatun manoma a jihar ba manomar na’ura mai kwakwalwa ba.

The post Kungiyar OYC sun gargadi Niger Delta Avengers appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.


Kungiyar OYC sun gargadi Niger Delta Avengers Reviewed by Olusola Bodunde on 08:01 Rating: 5

No comments:

Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us

All Rights Reserved by Naija News Live © 2014 - 2015
Powered By Blogger, Designed by Sweetheme

Contact Form

Name

Email *

Message *

Powered by Blogger.