Sports Betting

Trending

random

Obasanjo ya soki Gwamnoni kan katsalanda

– Obasanjo ya soki Gwamnoni kan katsalanda game da harkokin Kananan hukumoni.

 – Cif Olusegun Obasanjo ya caccaki Gwamnonin Najeriya.

 – Tsohon Shugaban Kasar Najeriyar Cif Obasanjo yace kutsen da Gwamnotocin Jihohi suke yi shi ke hana kananan hukumomi ci gaba a Najeriyar.

 – Obasanjo yace gwamnonin suna kawo matsala ga kasa wajen yin katsalandan ga sha’anonin Kananan hukumomi wanda yanzu sun zama ba su da wani tasiri.

 

Baba OBJ

 

 

 

 

 

 

Tsohon Shugaban Kasa Obasanjo, a ranar Talata 21 ga watan Yuni yake cewa kananan hukumomin Najeriya guda 774 sun zama bas u da wani amfani saboda katsalandan din da gwamnonin Jihohin Kasar suke yi masu a game da harkokin su.

 

Obasanjo yake cewa su Jihohin ba za su yarda Gwamnatin Tarayya ta rika yi masu irin wannan danniyar da suke yi ma kananun hukumomin su ba. Tsohon Shugaban Kasan Najeriyar Cif Obasanjo yayi wannan bayanin ne yayin da ‘yan kungiyar NULGE (Watau Kungiyar Ma’aikatan Kananan Hukumomin Kasar) suka ziyarce sa a gidan sa da ke ‘Presidential Hilltop Estate’ garin Abeokuta na Jihar Ogun. Shugaban Kungiyar, Ibraheem Khaleel yana neman taimakon tsohon Shugaba Obasanjo ne domin a samu Jihohi su kyale gwanotocin Kananan hukumomi sun yi aikin su. Shugaban Kungiyar yake kai kuka ga Obasanjo a ranar Laraba cewa: “Kaf Gwamnonin Najeriya, bai cire ko day aba, sun kassara kananan hukumomi, sun yi kace-nace kan harkokin su. Sai kuma aukin karkatar masu da kudi”

Sai dai Obasanjon yake fada masu shi yanzu babu abin da zai iya yi masu. Yake bayyana cewa lokacin da aka kafa gwamnatocin Kananan Hukumomi a shekarar 1976 (Wanda yana cikin Gwamnatin Sojan lokacin), an ba Kananan hukumomi damar su gudanar da ayyukan su. Yace amma yanzu, abin takaici gwamnatoci sun yi babakere kan harkokin kananan Hukumomi.

 

The post Obasanjo ya soki Gwamnoni kan katsalanda appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.


Obasanjo ya soki Gwamnoni kan katsalanda Reviewed by Olusola Bodunde on 08:01 Rating: 5

No comments:

Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us

All Rights Reserved by Naija News Live © 2014 - 2015
Powered By Blogger, Designed by Sweetheme

Contact Form

Name

Email *

Message *

Powered by Blogger.