Sports Betting

Trending

random

Duba jaddawalin gasar wasanni

– An fitar da cikakken jerin wasannin zagaye na-biyu na Gasar EURO 2016.

 – Babban wasan zagayen shi ne wanda za a kara tsakanin Kasar Spain, wadanda ke rike da kofi da kuma Kasar Italiya.

 – Za a buga wasannin a Ranar Asabar, Lahadi da Litinin dinnan.

Euro

An karkare wasannin gungu, yanzu za a shiga zagaye na gaba a gasar ta zakarun Nahiyar Turai watau EURO na Shekarar 2016. Kasar Ingila, da ta Jamhuriyar Ireland da Kasar Wales sun kai zagaye na gaba a gasar. A daf da karshen wasan ta da Kasar Italiya, Jamhuriyar Ireland din ta samu ta jefa kwallon da ya fito da ita.

Ga cikakken Jadawalin wasannin, hade da lokutta da rana a Kasa:

1. Kasar Poland za ta kara da Kasar Switzerland, a Ranar Asabar, 25 ga Watan Yuni da Karfe 2:00 na rana.

 2. Kasar Wales za ta hadu da ta Northern Ireland, a Ranar Asabar 25 ga watan Yuni da Karfe 5:00 na yamma.

 3. Kasar Croatia za ta fafata da Kasar Portugal, a Ranar Asabar 25 ga Watan Yuni da Karfe 8:00 na dare.

 4. Kasar Faransa za ta goge raini da Kasar Jamhuriyar Ireland, a Ranar Lahadi 26 ga Watan Yuni da Karfe 2:00 na rana.

 5. Kasar Jamus za ta buga da Kasar Sulobakiya, a Ranar Lahadi 26 ga Watan Yuni da Karfe 5:00 na yamma.

 6. Kasar Hungary za ta kara da Kasar Belgium, a Ranar Lahadi 26 ga Watan Yuni da Karfe 8:00 na dare.

 7. Kasar Italia za ta fafata da Kasar Spain, a Ranar Litinin 27 ga Watan Yuni da Karfe 5:00 na yamma.

 8. Kasar Ingila za ta hadu Kasar Iceland¸ a Ranar Litnin 27 ga Watan Yuni da Karfe 8:00 na dare.

The post Duba jaddawalin gasar wasanni appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.


Duba jaddawalin gasar wasanni Reviewed by Olusola Bodunde on 08:01 Rating: 5

No comments:

Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us

All Rights Reserved by Naija News Live © 2014 - 2015
Powered By Blogger, Designed by Sweetheme

Contact Form

Name

Email *

Message *

Powered by Blogger.