Sports Betting

Trending

random

Omisore ya fara bayani kan Naira Biliyan din EFCC

– Sanata Iyiola Omisore yace: Shi bai ma san Sambo Dasuki ba.

 – Hukumar EFCC tace ta ga wasu sama da Naira Biliyan daya a asusun wasu kamfunan sa.

 – Ana zargin Kudin na cikin Naira Biliyan 4 da Miliyan 700 din da Sanata Musiliu Obanikoro ya raba.

Senator-Iyiola-Omisore

 

 

 

 

 

 

Tsohon mataimakin Gwamnan Jihar Osun, Sanata Iyiola Omisore, yace shi bai karbi kudi ba daga wajen Sambo Dasuki, Tsohon mashawarcin Shugaban Kasa kan Harkar tsaro.

Da yake magana da ‘yan Jaridar PUNCH a ranar Laraba 22 ga wannan wata, tsohon mataimakin gwamnan da hukumar yaki da cin hancin kasar ta EFCC ke nema ruwa a jallo, yace kawai hukumar na nema ta bata masa suna ne. Yace shi tun da yake a duniya bai san Dasuki ba, bai taba zuwa ofishin sa ba. Omisore yace gwamnatin tarayya na amfani da hukumar EFCC ne kawai don ta muzguna masa, ta ci masa zarafi.

Omisore yake cewa: “An ce da na ci Naira miliyan 600, an dawo an ce kusan biliyan 2, yanzu kuma ance a’a, N1.3 ne. Da wanne zan ji?”

Hukumar dai ta EFCC ta bayyana cewa ta gano wasu asusun kamfani na Omisoren da aka ajiye kudi Naira biliyan daya da miliyan 300. Ana ganin Kudin na cikin Naira Biliyan 4 da Miliyan 700 din da Sanata Musiliu Obanikoro (Wani tsohon karamin ministan tsaron Kasar) ya raba.

Naira Biliyaan hudu da Miliyan 700 din dai sun fito ne daga asusun Ofisihin Mai ba Shugaban Kasa shawara kan tsaro a shekarar 2014, daga nan aka jefa su asusun wani kamfani ‘Sylvan McNamara’ a bankin Diamond Bank. Wanda Obanikoro da ‘ya ‘yan sa; Gbolahan da Babajide suna daga cikin masu wannan kamfani. Sanata Omisore dai yace EFCC din ba ta isa ba! Ya maka ta kara a Babban Kotun Tarayyar Najeriya na Abuja, yana bukatar da a biya sa Naira biliyan 10 na bata masa suna, kuma yana rokon Kotu ta sa kar a kara binciken Sa.

The post Omisore ya fara bayani kan Naira Biliyan din EFCC appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.


Omisore ya fara bayani kan Naira Biliyan din EFCC Reviewed by Olusola Bodunde on 08:01 Rating: 5

No comments:

Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us

All Rights Reserved by Naija News Live © 2014 - 2015
Powered By Blogger, Designed by Sweetheme

Contact Form

Name

Email *

Message *

Powered by Blogger.