Watan Ramadana: Makantan Gaske
– Idanuwa hasken rayuwa
– Duk mutumin da ya makance bayan ya kasance mai gani ya tambaya kanshi meya sa?
Amma akwai makanta na din-din-din a ranar tashin Al Kiyama ga wanda yayi sakaci da ayoyin Allah, wanda shi zamuyi Magana akai. Wannan na nufin mutum da bai kaunar sauraron kalmomin alkur’ani da hadisan manzon Allah “tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi” zai fuskanci makantan ranar tashin Al-kiyama
Zamu samu bayanin wannan karara a cikin Alkur’ani Mai girma a Surah ta 20,Aya 124-127 inda Allah madaukakin sarki ya ce: “ Duk wanda ya baude daga ambato na, to ya sani ,zai fuskanci rayuwa mai tsanani, kuma zamu tarashi ranar alkiyama makaho”
“Sannan sai yace ce,(Allah) saboda meye zaka tashe ni makaho bayan na kasance mai gani”
“Sai Allah yace masa: haka ka manta da ayoyinmu, shi yasa yau aka mantar da kai”
Sai Allah yace: “Haka zamu sakamantawa wadanda suka wuce gona da iri kuma yak i imani da ayoyin ubangijin shi kuma azaban lahira mafi zafi ce da wanzuwa”
KU KARANTA : Abubuwa 5 masu muhimmanci a 10 karshen Ramadana
A karshe, muna ba dukkan musulmai shawara da su nisanci duk abinda zai hana su sauraron kalmomin Allah. Watan ramadana;asha ruwa lafiya
The post Watan Ramadana: Makantan Gaske appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.
No comments:
Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us