Hukumar ‘yan sanda tayi bayani game da hari a Lagos
-Hukumar ‘yan sandan jihar Lagos tayi bayani game da tsagerun da suka kai hari ranar 27, Yuli
-Hukumar ta bayyana yadda ta hana tsagerun kaima mazauna unguwar Igando hari
Hukumar ‘yan sandan jihar Lagos ta bayyana yadda ta dakile kaima mazauna unguwar Igando hari ranar Talata 26, Yuli daga wasu tsageru da ba’a sani ba. Mai magana da yawun ‘yan sanda Mrs Dolapo Badmos, ta tabbbatar da haka ga dillalin labaru ta kasa (NAN).
KU KARANTA : Tsageru sun kashe yan sanda 6 a Legas
Ta ci gaba da cewa “wani gungun mutane sun abka ma mazauna unguwar Igando da safiyar Talata. Jami’an mu da aka aje a muhimman wurare a unguwar sun sami labari sukayi sauri suka fatattake su. A halin yanzu hankali ya kwanta”.
The post Hukumar ‘yan sanda tayi bayani game da hari a Lagos appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.
No comments:
Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us